Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ma'aikatar kudi ta Amurka a jiya Laraba ta sanar da kakaba takunkumi kan wani mutum da kamfanonin da ke da alaka da shi saboda ba da taimako ga shirin makami mai linzami na Iran.
A cikin sanarwar da ta fitar, ma'aikatar kudi ta kasar ta ce sabbin takunkuman sun shafi kamfanonin da suka sayo kayayyakin da ke da alaka da makami mai linzami ga rukunin dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) da ke da alhakin gudanar da bincike da kuma kera makaman ballistic.
Lavrov ya ce Rasha za ta hada kai da Iran wajen daukar matakai na zahiri a kokarin kaucewa takunkumin da kasashen yamma suka kakaba mata.
Kalaman na zuwa ne a daidai lokacin da Rasha take fuskantar takunkuman kasashen yammacin turai, tun bayan da Moscow ta kaddamar da farmakin soji a Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu.
Amurka da kawayenta na Turai ne suka jagoranci kakabawa Rasha takunkumi.
Har ila yau Iran ta fuskanci wasu takunkuman Amurka, wanda Washington ta kakaba mata, bayan da tsohon shugaban kasar Donald Trump ya ayyana ficewa daga yarjejeniyar hadin gwiwa (JCPOA), wanda aka fi sani da yarjejeniyar shirin Iran na nukiliya a watan Mayun 2018.
342/